Pochettino ya bar chelsea bisa sharuɗɗan juna

Kociyan Chelsea, Mauricio Pochettino ya bar ƙungiyar bayan da suka amince su raga gari a tsakaninsu, bayan kaka daya da ya yi a Stamford Bridge.

Pochettino, mai shekara 52, ya karbi aikin horar da Chelsea ranar 1 ga watan Yuli, kan kwantiragin kaka biyu da cewar za a kara masa shekara daya idan ya taka rawar gani.

Ɗan kasar Argentina ya fuskanci kalubale a wasannin zagayen farko a kakar bana, daga baya ya kara ƙwazo da ta kai ta kare a mataki na shida a Premier League.

Haka kuma Chelsea ce ta yi ta biyu a Carabao Cup a bana da kai wa zagayen daf da karshe a FA Cup.

”Ina godiya ga mahukuntan Chelsea da daraktan wasannin ƙungiyar bisa damar da suka bani na horar da ita” in ji Pochettino.

”Yanzu dai ƙungiyar ta hau kan turba da za ta taka rawar gani a Premier League a badi da gasar zakarun Turai a shekaru masu zuwa.”

Shi ne kociya na uku da aka kora a kungiyar, bayan Thomas Tuchel da Graham Potter, tun bayan Todd Boehly da Clearlake Capital suka sayi ƙungiyar a cikin watan Mayun 2022.

“A madadin kowa a Chelsea, muna godiya ga Mauricio kan yadda ya gudanar da aiki da rawar da ya taka.” in ji daraktan wasanni. Laurence Stewart da kuma Paul Winstanley.

“Za mu ci gaba da yi masa maraba a duk lokacin da ya ziyarci Stamford Bridge a kowanne lokaci, muna masa fatan alheri a aikinsa na horar da tamaula da zai yi nan gaba.”

Masu taimakawa kociyan da ya hada da Jesus Perez da Miguel d’Agostino da Toni Jimenez da Sebastiano Pochettino duk sun bar Stamford Bridge

0 Shares

Leave a ReplyCancel reply